Sarkin Kano Ya Hana Gidan Rediyon Freedom Yayata Batun Bidiyon Ganduje


Mai martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya hana fitaccen gidan Rediyo mai zaman kansa na jihar Kano (Freedom Radio) yayata bidiyon Gwamna Abdullahi Umar Ganduje.

Bidiyon da ake zargin Gwamnan ya karbi cin hanci da rashawa, ya zama babban abin tattaunawa a kafafen sada zumunta na zamani.

A shirin INDA RANKA wanda shahararren dan jarida Nasiru Salisu Zango ke gabatarwa, ana ragargazar mutane ne a duk wani sha’ani na rashin gaskiya. An kawo dandanon labarin bayyanar bidiyon, amma a cikin Labaran an ki bayyana komai ba a kuma ce a biyo bashin labarin ba.

Majiyarmu ta gano daga kwakkwarar majiya a gidan rediyon cewa, mai Martaba SARKI Muhammadu Sanusi II ne ya nemi alfarma aka dakatar.

“Mai Martaba Sarki ne kadai ya ke da wannan alfarmar kaf jihar Kano. Sai kuma wasu Malamai da ba a rasa ba. Amma ko mai gidan Rediyon bai isa ya hana Zango daukar labari ba.” Inji majiyar.


Like it? Share with your friends!

-2
92 shares, -2 points

Comments 1

Your email address will not be published.

You may also like