Sarkin Gwoza Ya Koma Gida Bayan Shekara Biyar Da Yin Gudun Hijira


Mai Martaba Sarkin Gwoza Alhaji Mohammad Shehu Idrissa ya koma garin sa Gwoza tun bayan gudun hijira da yayi na tsawon shekaru 5 sakamakon rikicin Boko Haram a lokacin da Boko Haram suka kwace garin na Gwoza.

Mataimakin Gwamnan Borno Hon. Umar Usman Kadafur ne ya jagoranci komawar tare rakiyar Sanatan Borno ta kudu Sanata Mohammed Ali Ndume da suran manyan jami’an Gwamnati.

Komawar Basaraken baya rasa nasaba da irin zaman lafiya da kwanciyar hankali da aka samu kuma ake ci gaba da samu a jahar Borno.


Like it? Share with your friends!

0

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like