Sarkin Anka: Yakamata Buhari ya kori ministan tsaro


Sarkin Anka, Attahiru Ahmad wanda shine shugaban majalisar sarakunan jihar Zamfara ya ce kamata yayi shugaban kasa Muhammad Buhari ya kori ministan tsaro,Mannir Dan-Ali daga bakin aiki.

Mai martaba sarkin ya yi wannan kalami ne a wata tattaunawa da jaridar The Punch a matsayin martani kan zargin da ministan ya yi cewa wasu daga cikin masu rike da sarauta a jihar suna hada baki da barayi yan bindiga da suka addabi jihar.

Sarkin ya ce kalaman zargin da ministan ya yi suna da nauyi sosai inda ya ce Dan-Ali wanda dan asalin karamar hukumar Birnin Magaji ne dake jihar kamata ya yi ya koma can da zama a matsayin wani ɓangare na shawo kan matsalar yan bindigar da suka addabi jihar.

“Abune mai munin gaske matuka ace ministan tsaro yana zargin mu da taimakawa yan bindiga.Idan da a wata kasar ne da tuni sai an kori ministan saboda zargin na shi yana da nauyi sosai.

“Ya ce ba wai iyaka jihar Zamfara ne ba kaɗai sarakuna gargajiya ke taimakawa barayi yan bindiga ba har ma da na sauran sassan arewacin Najeriya,”

“Amma munyi shiru saboda daga cikin mu ya fito.Kaje karamar hukumarsa kaga abin da yake faruwa.Saboda haka a matsayinsa na ministan tsaro.kamata ya yi ya koma can,” ya ce

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like