Sarki Sunusi ya kai ziyara asibitin yara na Hasiya Bayero dake Kano


Sarki Kano, Muhammad Sunusi II, ya kai ziyara asibitin kananan yara na Hasiya Bayero.

Sarkin wanda ya samu rakiyar wasu daga cikin fadawansa da kuma yan majalisarsa.

Mai martaba sarkin ya yi amfani da ziyarar wajen rabawa majinyata kayan sallah.

Da yawa daga cikin masu jinyar yaransu a asibitin sun yaba da ziyarar da sarkin ya kai musu kana suka gode masa bisa wannan abin alkhairi.

Ziyarar marasa lafiya dake asibitocin jihar abu ne da sarkin ya saba gudanarwa.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like