Sarakunan Zamfara ga ministan tsaro: Ka bayyana sunan masu hada kai da barayi


Majalisar sarkunan jihar Zamfara tayi kira ga ministan tsaro, Mannir Dan Ali da ya gaggauta bayyana sunan masu rike da sarautun gargajiya dake hada kai da barayi a jihar.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwar bayan taro mai dauke da sahannun,sarkin Anka shugaban majalisar sarakunan jihar, Alhaji Attahiru Muhammad Ahmad.

Mai martaba sarkin, Bungudu Alhaji Hassan Attahiru shine ya karanta jawabin bayan kammala taron gaggawa na majalisar a Gusau.

Sarakunan sun ce gazawar bayyana sunan wadanda suke da hannu a zargin zai sa kalaman ministan su zama na karya da yayi domin bata sunan sarakunan.


Like it? Share with your friends!

-1
110 shares, -1 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like