Saraki yaki magana da yan jarida bayan ganawarsa da Babangida


Shugaban majalisar dattawa, Abubakar Bukola Saraki ya ki magana da yan jaridu bayan da ya yi wata ganawar sirri da tsohon shugaban kasa, Ibrahim Badamasi Babangida a gidansa dake Minna.

Saraki ya isa gidan Babangida da misalin ƙarfe 4:10 ya kuma bar gidan da karfe 5:50 na yamma.

Lokacin da ya isa filin jirgin saman Minna yaki kula yan jarida da suke son yi masa tambayoyi.

Kamfanin. Dillancin Labaran Najeriya NAN ya ruwaito cewa Saraki ya isa gidan tsohon shugaban kasar a wani ayarin motoci guda tara.

Ziyarar tasa ta biyo bayan taron manema labarai da ya kira kan hana shiga majalisar tarayya da jami’an tsaron DSS suka yi.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like