Saraki ya yi ganawar sirri da Obasanjo


Shugaban majalisar dattawa Abubakar Bukola Saraki ya ziyarci tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo.

Bisa rakiyar wasu makusantansa Saraki ya shiga ganawar sirri da tsohon shugaban kasar.

Ganawar na zuwa ne kwanaki biyar bayan ziyarar da ya kai Minna babban birnin jihar Neja inda ya gana da tsohon shugaban kasa, Ibrahim Badamasi Babangida.

Ziyarar ta Saraki ga wasu masu fada aji a Najeriya na zuwa ne bayan ya nuna alamun yin takarar shugaban kasa.

Dukkannin tsofaffin shugabannin kasar sun yi kira ga shugaba Buhari da ya hakura da mulki a karo na biyu.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like