Saraki ya yabawa shugaba Buhari da namijin kokarin da ya yi wurin ceto rayuwar Zainab Aliyu


Shugaban majalisar dattawa, Sanata Bukola Saraki, ya yaba da kokarin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi ta fannin diflomasiyya wurin ganin an sako Zainab Aliyu da Ibrahim Abubakar daga gidan yarin kasar Saudiyya, bisa zargin da ake musu na shiga da miyagun kwayoyi kasar.

Mista Saraki, wanda ya yi yabon na shi a lokacin da Sanata Kabiru Gaya ya ta so da zancen a majalisa ranar Talata, ya ce sakin su ba karamin sauki ba ne ga ‘yan Najeriya.
Saraki ya yabawa shugaba Buhari da namijin kokarin da ya yi wurin ceto rayuwar Zainab Aliyu

Zainab Aliyu wacce ta ke daliba ce a Jami’ar Maitama Sule, da ke Kano, da kuma Ibrahim Abubakar, an kama su ne a kasar Saudiyya, bisa zargin shiga kasar da miyagun kwayoyi, inda aka kamata a filin tashi da saukar jiragen sama na Prince Mohammed Bin Abdulaziz da ke Madina, saboda an gano kwayar a cikin jakarta.

Zainab, ta yi yunkurin kare kanta, inda ta bayyana cewa saka mata kwayar aka yi a cikin jakarta.
Bugu da kari, an kama Abubakar shi ma a kasar da laifin shiga da kwaya.

Yayin da yake magana akan doka ta 43 ta majalisar dattijai, Mista Gaya ya ce ya kamata a yabawa shugaban kasa Muhammadu Buhari, Majalisar Dattijai, da duk wadanda suka ba da gudummawa wajen sakin su.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito cewa Sakataren Ma’aikatar Harkokin Waje, Mustapha Sulaiman, wanda ya tabbatar da sakin su, ya ce an sake sune sakamakon an bi hanya ta diflomasiyya tsakanin gwamnatin Najeriya da ta Saudiyya.


Like it? Share with your friends!

1
107 shares, 1 point

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like