Saraki ya rantsar da sanatocin biyu ƴan jam’iyar APC


Shugaban majalisar dattawa, Abubakar Bukola Saraki ya rantsar da sanatoci biyu da aka zaba karkashin jam’iyar APC.

Sanatocin sune Ahmed Babba Kaita daga jihar Katsina da kuma Lawal Yahaya Gumau daga jihar Bauchi.

Mutanen biyu sune suka lashe zaɓen cike gurbi da hukumar zabe ta INEC ta gudanar biyo bayan mutuwar Sanata Ali Wakili mai wakiltar mazabar Bauchi ta kudu da kuma Sanata Mustapha Bukar dake wakiltar mazabar arewacin Katsina a majalisar.

Hukumar zabe ta kasa INEC ta gudanar da zaɓen cike gurbi a mazabun biyu inda jam’iyar APC tayi nasara da gagarumin rinjaye.

Mustapha Bukar ya rasu cikin watan Afirilu ya yin da Ali Wakili ya rasu cikin watan Mayu.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like