Sannu A Hankali Za Mu Cire Tallafin Man Fetur – Gwamnatin Tarayya


Ministar kudin Nijeriya, Zainab Ahmad, ta ce sannu a hankali gwamnatin tarayya za ta cire tallafin man fetur.

Hajiya Zainab ta bayyana hakan yayin da take maida martani ga shawarar asusun bayar da lamuni na IMF na bukatar Nijeriya ta yi duba akan iyuwar cire tallafin man fetur domin zuba kudin a cikin ayyukan cigaban kasa.

A nata bangaren, ministar kudin ta nuna amincewarta ga matakin asusun bayar da lamunin na IMF, amma ta ce gwamnatin na bukatar daukar wasu matakai kafin cire tallafin.

Ministar ta ce shawar da IMF ya bayar shawara ce mai kyau, amma muna cikin wani yanayi da ba za mu tashi katsam a rana daya mu ce an cire tallafi ba. Dole a ilimantar da ‘yan Nijeriya tare da wayar da su a kan amfanin cire tallafin.


Like it? Share with your friends!

1
84 shares, 1 point

Comments 1

Your email address will not be published.

You may also like