Sanatocin APC sama da 30 na goyon bayan Ndume ya zama shugaban majalisar dattawa


Aƙalla zababbun sanatoci 36 da suka fito daga jam’iyar APC ne ke goyon bayan sanata Ali Ndume a takarar da yake ta zama shugaban majalisar dattawa.

Wani sanata da ya fito daga yankin arewa shine ya bayyana haka a wurin taron sanin makamar aiki da aka shiryawa zababbun yan majalisar a otal din Trancorp Hilton dake birnin tarayya Abuja.

Sanatan ya bayyana haka ne ranar Talata lokacin da yake tatttaunawa da wasu yan jarida.

Duk da cewa jam’iyar APC ta nuna goyon bayanta ga takarar, Ahmad Lawal amma Ndume ya dage kan cewa sai ya shiga takarar neman shugabancin majalisar.

Zaɓaɓɓen sanatan ya ce wasu daga cikinsu ba suji dadin yadda aka raba shugabancin kwamitocin majalisar masu romo ba a tsakanin magoya bayan Ahmad Lawan.

“Akwai sanatoci 36 dake goyon bayan takarar Ndume saboda munajin haushin yadda abubuwa suke gudana kan batun shugabancin majalisar dattawan,”ya ce


Like it? Share with your friends!

-3
97 shares, -3 points

Comments 1

Your email address will not be published.

You may also like