Sanatoci sun nemi Buhari ya kori manyan hafsoshin tsaro


Majalisar dattawa tayi kira ga shugaban kasa, Muhammad Buhari da ya sallami shugabannin rundunar tsaron kasar.

Kiran na majalisar na zuwa ne biyo bayan harin da mayakan Boko Haram suka kai a Zabarmari inda suka kashe manoma masu yawa da kawo yanzu ba a san adadinsu ba.

Wannan kiran na baya-bayan nan kari ne kan kiraye-kirayen da majalisar ta sha yi ga shugaban kasar na neman a kori manyan hafsoshin tsaron ƙasar.

Sai dai mutane da dama na ganin cewa shugaban kasar zai yi kunnen uwar shegu da kiran na yan majalisar dattawan.


Like it? Share with your friends!

0

Comments 2

Your email address will not be published.

You may also like