Sanata Oduah ta sauya sheka daga jam’iyar PDP ya zuwa APGA


Tsohuwar ministan harkokin sufurin jiragen sama, Sanata Stella Oduah, dake wakiltar mazabar Arewacin Anambra, a hukumance ta sauya sheka daga jam’iyar PDP ya zuwa jam’iyar APGA.

Oduah wacce ta samu jagorancin, Sanata Victor Umeh, ya zuwa hedikwatar uwar jam’iyar ta kasa inda suka samu tarba daga shugaban jam’iyyar, Dr. Victor Oye.

Sauya shekar tata shine ya kawo yawan santocin da jam’iyar take da su ya zuwa biyu bayan yan majalisar wakilai ta tarayya guda shida.

Sauya shekaca tsakanin jam’iyyu abune da ya zama ruwan dare a tsakanin yan siyasar Najeriya.

Masana da dama na ganin hakan ka iya zama illa ga dimakwaradiyar Najeriya.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like