Sanata daga Filato ya mutu


Ignatius Longjan, sanata mai wakiltar mazabar kudancin Filato ya mutu.

Rahotanni sun bayyana cewa sanatan ya mutu ne sakamakon wata cuta da ba a bayyana ta ba wacce ya dade yana fama da ita. Ya mutu yana da shekaru 75.

Wata majiya dake iyalinsa ta bayyana cewa ya mutu ne a wani asibiti dake Abuja a daren ranar Litinin.

Wannan shi ne karo na biyu da ake samun rasuwar wani sanata a majalisar dattawa tun bayan da aka ƙaddamar da majalisar a watan Yunin shekarar da ta wuce.

Leave your vote


Like it? Share with your friends!

-1
42 shares, -1 points

You may also like

Log In

Forgot password?

Forgot password?

Enter your account data and we will send you a link to reset your password.

Your password reset link appears to be invalid or expired.

Log in

Privacy Policy

Add to Collection

No Collections

Here you'll find all collections you've created before.