Samar Da Dakarun Tsaron Daji Zai Magance Matsalar Tsaron Najeriya
Wata sanarwar gwamnati ta ruwaito gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje na cewa tuni gwamnati ta kafa kwamiti na musamman da ya kunshi kwararru da dukkanin masu ruwa da tsaki domin tabbatar da nasarar da aka sanya a gaba.

Wannan mataki dai na kidayar Fulani a Kano na zuwa ne makonni kalilan bayan da rundunar ‘yan sandan jihar ta bullo da tsarin hana Fulani shiga jihar Kano ba tare da takardar shaida ba, a cewar kwamishinan ‘yan sanda Sama’ila Dikko.

Ko da yake, gwamnati na daukar irin wadannan matakai, amma daga cikin masana lamuran tsaro akwai masu ra’ayin cewa samar da dakarun tsaron daji da ake kira “Forest Marshall” ne kawai ka iya kawo karshen fitinar ‘yan ta’adda a Najeriya.

Hakan dai na zuwa ne a dai dai lokacin da rundunar sojojin ruwa ta Najeriya ke bayyana aniyyar kafa kwalejin horas da Jami’anta a Kano.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:


Leave your vote

You may also like

Log In

Forgot password?

Forgot password?

Enter your account data and we will send you a link to reset your password.

Your password reset link appears to be invalid or expired.

Log in

Privacy Policy

Add to Collection

No Collections

Here you'll find all collections you've created before.