Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta ce gwamnatin kasar za ta yi duk abin da ya dace wajen taimakon yankunan kasar da suka tagaiyara sakamakon ambaliyar ruwan da aka samu. Ta kuma yaba wa masu aikin ceto yayin ziyarar da ta kai yankunan a wannan Lahadi da ta gabata, sannan ta ce zai dauki lokaci kafin lamura su koma daidai.

Ambaliyar ta halaka fiye da mutane 150 yayin da wasu da dama suka bace ake ci gaba da nema. Tuni wannan bala’in ya sauya batun yakin neman zaben watan Satumba mai zuwa lokacin da Jamuwasa za su kada kuri’a a zaben kasa baki daya, wanda zai kawo karshen mulkin Angela Merkel na shekaru 16.