Sakataren PDP na jihar Kebbi ya koma APC


Sakataren jam’iyar PDP na jihar Kebbi, Alhaji Muhammad Sakaba ya sauya sheka ya zuwa jam’iyar APC tare da magoya bayansa.

Sakaba wanda a gwamna, Abubakar Atiku Bagudu ya karbe shi ya sanar da sauya shekar tasa a birnin Kebbi ranar Laraba .

Tsohon sakataren ya bayyana cewa ya sauya shekar ne saboda yadda da yayi da shugaban kasa Muhammad Buhari da kuma Atiku Bagudu inda yace sunyi iya kokarinsu cikin shekaru 4 wajen ciyar da jihar gaba dama Najeriya baki daya.

Ya kuma yi alkawarin tattara dubban magoya bayansa domin tattabar da sake zaben shugaba Buhari da Bagudu a zabe mai zuwa.

Anasa jawabin Bagudu ya godewa Sakaba kan yadda ya yaba da salon mulkin gwamnatin Buhari.


Like it? Share with your friends!

-1
66 shares, -1 points

Comments 1

Your email address will not be published.

You may also like