Sakamakon gwaji ya nuna gwamnan Bauchi ya warke daga cutar Coronavirus


Gwajin da aka yi wa gwamnan jihar Bauchi, Bala Muhammad ya nuna cewa baya dauke da cutar Coronavirus mako biyu bayan da ya kamu da cutar.

Idan za a iya tunawa gwamnan ya sanar da cewa zai killace kansa bayan da yayi cudanya da dan gidan tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar wanda aka samu yana dauke da cutar.

Har ila yau an samu wasu makusantan gwamnan su biyu da suka kamu da cutar.

Wata majiya mai tushe dake gidan gwamnatin jihar, ta fadawa jaridar Daily Nigerian cewa gwamnan ya warke daga cutar kuma nan bada dadewa zai fito daga wurin da aka killace shi a gidan gwamnatin jihar.


Like it? Share with your friends!

0

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like