Safarar Bil’adama: An Bankado Masana’antar Sayar Da Jarirai A Jihar Filato.


Hukumomin tsaro a jihar Filato sun ce, sun kama wasu mutane da suka hada maza da mata cikin su har da wata mai ciki dake gab da haihuwan da ake zargi da safarar jarirai.

Hukumomi sun ce mutanen da aka kama dai sun hada da ‘yan mata da akan yi wa ciki su haihu domin sayar da jariran da kuma wasu maza da ake zargi da ajiye ‘yan matan suna yi musu ciki.

Kwamandan Rundunar tsaro ta musamman da ke aikin kiyaye zaman lafiya a jihar ta Filato, Manjo Janar Nicolas Rogers, ya bayanna haka ckin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a Jos babban birnin jihar Filato.

A wani labarin kuma, Hukumar yaki da masu sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Na jeriya, NDLEA, ta kama wani mutum da kwanso 73 na hodar ibilis, yayin da yake yunkurin fita daga Nijeriya zuwa Dubai Hadaddiyar Daular Larabawa.

An kama mutumin mai shekara 49 ne a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe dake Abuja a yayin da ake gudanar da bincike.


Like it? Share with your friends!

-2
96 shares, -2 points

Comments 2

Your email address will not be published.

You may also like