Sabon Lale: El-Rufa’i Ya Soke Zaɓen Sarkin Zazzau


Sakataren Gwamnatin Jihar Kaduna, Balarabe Abbas Lawal, ya bayyana cewa manyan hakiman da ke zaɓen sarkin Zazzau za su fara sabon aikin zaɓen sabon sarkin Zazzau na 19 a daular Fulani.

Sakataren gwamnatin ya bayyana cewa Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa’i ne ya bayar da umarnin sake aikin zaɓen sarkin biyo bayan soke zaɓen da masu zaɓen sarkin suka yi da farko da ya yi.

Mashawarci na musamman ga gwamnan kan yaɗa labarai, Muyiwa Adeleye, ya bayyana cewa ɗaya daga cikin ‘yan takarar sarkin, Bunun Zazzau, ya yi ƙorafin cewa bai samu damar bayar da takardar takararsa ba “domin an bayyana masa cewa an rufe karɓa.”

“Shi ma Sarkin Dajin zazzau ya koka a kan cire shi da aka yi daga jerin ‘yan takara. An kuma gano cewa masu zaɓen sarkin sun tantance wasu ‘yan takara guda biyu ran 24 ga watan Satumba, 2020 ba tare da ganin takardunsu ba, wanda sai washegarin ranar suka karɓa.

Ya kuma da ƙara cewa gwamnatin jihar ta bayyana cewa ba ƙaramin kuskure ba ne ɓullar da rahoton aikin zaɓen sarkin da aka yi a ranar 24 ga watan Satumba 2020 ya yi tun kafin gwamnan jihar ya karɓa.

“A yanzu masu zaɓen sarkin a za su sake haɗuwa domin tantance gabaɗayan ‘yan takara sha ukun da suka nuna buƙata daga dukkan gidajen da ke mulkin masarautar, ciki har da mutane biyun da aka cire a zaɓen farko.

“Cikin gaggawa kuma za a damƙa wa gwamnan rahoton tantancewar domin ya duba.”


Like it? Share with your friends!

0

You may also like