Sabbin Sarakuna: Mun yiwa dokar garambawul, babu mai iya canja ta – Ganduje


Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewa garambawul din da aka yiwa dokar nadi da sauke sarakuna a shekarar 2019 ba zai warwaru ba, saboda yadda aka yiwa dokar tankade da rairaya.

Ganduje ya fadi hakan ne yayin bikin nuna jin dadi da yi masa godiya da sabbin sarakunan Rano, Bichi da Karaye suka shirya.

Gwamna Ganduje ya bukaci dukkan hakimai da manyan limamai dake karkashin sabbin masarautun, da su yi musu mubaya’a ranar Lahadi.

Ya yi kira ga sabbin sarakunan da su mayar da hankali wajen bawa jama’a jama’a karfin rungumar noman rani da na damina, kiwon lafiya, da neman ilimi.

Yace ” Ku tabbatar jama’ar ku sun tura yaran su makaranta, mata kuma sun ziyarci asibiti a lokacin da suka samu juna biyu.
“Mun gano shirin wasu batagari na gudanar da zanga-zanga. Zasu yi hakan ne domin haddasa rashin zaman lafiya a Kano, amma hakan ko kadan ba zai saka mu canja ra’ayinmu a kan kirkirar sabbin masarautun ba.

“Mun kirkiri sabbin sarakunan yanka ne domin rage wa masarautar Kano nauyin dake kan ta. Nauyin ya yiwa masarautar yawa, hakan ne ma ya sa muka kirkiri wasu domin a rage mata nauyi ,” a cewar Ganduje.

Sannan ya cigaba da cewa; ” kirkirar sabbin masarautun tamkar sake waiwayar tarihi ne. Wannan ba wani sabon abu ba ne a Kano, hakan ta taba kasancewa a baya.

“Mun kirkiri sabbin masarautun ne domin amsa bukatar mutanen mu. Na tabbata yin hakan zai kawo cigaba cikin sauri ga yankunan karkara. ” a cewar Ganduje


Like it? Share with your friends!

1
91 shares, 1 point

Comments 1

Your email address will not be published.

You may also like