Rundunar Sojin Najeriya Ta Gargadi Masu Rura Wutar Rikici
A hirar shi da Muryar Amurka, Janaral Farouk Yahaya ya jaddada cewa rundunar sojin kasar zataci gaba da yin biyayya ga kundin tsarin mulkin da Najeriya, inda ya tabbatarwa yan kasar cewa hafsoshi da sojojikn kasar baki daya za suci gaba da kare yanci da diyaucin Najeriya.

Babban Hafsan hafsoshin sojojin Najeriyar kazalika ya kuma ce zasu ci gaba da aiki tare da sauran rundunonin mayaka da sauran jami’an tsaro wajen taimakawa hukumomin fararen hula don samar da kyakkyawan yanayin gudanar da babban zaben.

Bugu da kari Shugaban sojojin ya kuma nemi sojojin da su taka rawar da ta dace wajen bin ka’idoji da tanaje tanajen da aka tsara yayin da suke aikin tallafawa samar da tsaro lokacin gudanar da babban zaben na shekara ta dubu biyu da ashirin da uku.

Masu ruwa da tsaki irinsu Bashir Dan musa na ganin wannan gargadin da rundunar mayakan ke aikewa masu rura wutar rikicin yazo daidai lokacin da ya dace musamman ganin yanzu dakarun na samun nasara kwarai da gaske akan masu tafka ta’asa a kasar.

Dan Musa yace yanzu ba lokacin yin batanci ko rura wutar rikici ba ne, don haka yunkurin sojojin ba ko shakka zai taimaka wajen samar da sauki sosai kan matsalar tsaron wanda hakan ka iya taimakawa wajen gudanar da zabubbukan na badi idan Allah ya kaimu cikin kwanciyar hankali.

Yanzu dai abin jira a gani shine irin rawar da sojin zasu taka wajen samar da kwanciyar hankali a zabubbukan na shekara mai kamawa musamman ganin sassa daban daban na kasar na fama da tarin kalubalen tsaro.

Saurari rahoton cikin sauti:


Leave your vote

You may also like

Log In

Forgot password?

Forgot password?

Enter your account data and we will send you a link to reset your password.

Your password reset link appears to be invalid or expired.

Log in

Privacy Policy

Add to Collection

No Collections

Here you'll find all collections you've created before.

omg