Rundunar sojan sama ta kori sojan da aka samu da aikata fyade kan yar gudun hijira mai shekaru 14


Wata kotun soja dake zamanta a Maiduguri ta zartar da hukunci kan wani sojan saman Najeriya mai suna, Martins Owerem bayan da aka same shi da aikata laifin yin lalata da wata yarinya yar gudun hijira mai shekaru 14.

Owerem ya aikata laifin ne lokacin da yake jagorantar bataliyar sojoji na musamman dake aiki a kusa da sansanin yan gudun hijira na Bakassi, a shekarar 2018.

Tunda fari lauya me kara, Aminu Mairuwa ya fadawa kotun cewa mutumin da ake zargi ranar 29 ga watan Satumba 2018 lokacin da suke gudanar da sintiri a unguwar Kawon Jiya dake wajen birnin Maiduguri sun kama wasu mata dake neman itace inda suka fake da cewa sun shiga wurin da aka hana shiga.

Mairuwa ya ce daganan mai laifin ya dauki daya daga cikin yan matan inda ya shiga da ita cikin daji yayi mata fyade.

Amma lauyansa, Abbas Abba ya nemi da a yiwa mai laifin sassauci duba da ya bautawa kasa da kuma gudunmawar da ya bayar a yaki da ta’addanci a yankin arewa maso gabas.

Da yanke yanke hukuncin jagoran alkalan kotun, Yakubu Auta ya ce kotun ta samu Owerem da aikata laifuka biyu da ake tuhumarsa da aikatawa fyade da kuma cin zarafi.

Comments 1

Your email address will not be published.

You may also like