Ko da yake shugaban na Faransa  ya ce zasu janye daga aikin na yaki da ta’addanci a cikin rundunar, amma ya ce sojojinsu za su ci gaba da aiki a cikin rundunar soji ta hadin gwwiwa tsakanin turai da kasashen Afirka Takuba domin yakin da ta’addanci. Faransa na da sojoji sama da dubu biyar a cikin rundunar ta Barkhane ada aka kafa tun a shekara ta 2014 wacce ta yi nasara kwato yankin arewacin Mali da kungiyar ‘yan ta’adda ta kwaci iko da shi. Fransa ta yanke shawarar dakatar da ayyukan sojojinta ne a Mali bayan juyin mulki da sojojin suka yi na kiffar da gwamnatin wucin gadi ta farar hula a makonnin da suka gabata.