Rufe iyakoki: Man fetur da ake amfani da shi a Adamawa ya ragu da kaso 70


Shugaban hukumar DPR dake lura da albarkatun mai a jihar Adamawa, Chiroma Adamu ya ce adadin yawan tankokin mai dake shiga jihar a kullum ya ragu daga 100 ya zuwa 40 zuwa 30.

Chiroma ya fadi haka lokacin da ya kai ziyara kauyen Bele dake karamar hukumar Maiha da kuma kauyen Gurin dake karamar hukumar Fufore ta jihar.

Ya ce rufe kan iyakoki da aka yi ya kawo karshen cuwa-cuwar mai da ake a garuruwan dake kan iyaka.

“Kafin wannan rufe iyakar yawan tankokin mai da muke samu a Adamawa ya kai har 100 a rana amma a yau ya yi kasa tsakanin 30 zuwa 40. Hakan wata manuniya ce dake nuna cewa man fetur baya samun fita daga kasarnan.” Ya ce


Like it? Share with your friends!

0

Comments 21

You may also like