Ronaldo Ya Saka Rigar Kungiyar Kwallon Kafa Ta Nigeria Domin Nuna Goyon Bayansa ga Ƙungiyar


Shahararren dan wasan gaba na Real Madrid wanda kuma dan asalin kasar Portugal ne, ya sanya rigar Najeriya wacce ta kasance Riga mafi kyawu a gasar kwallon kafan duniya dayake gudana a ƙasar rasha a halin yanzu.

Dan Wasan wanda tuni ya zura kwallaye hudu a kakar wasan wanda ya kasance wanda yafi kowa zura kwallaye tare da dan wasan gaba na kasar Belgium wato Romelu Lukaku.

Ya Sanya rigar Najeriya ne domin nuna goyon bayan sa da kungiyar ta Super Eagles wanda mutanen ke ganin yayi hakan ne domin kishiyar sa na kasar Argentina wato lionel Messi.

Super Eagles dai zata buga wasa sa kasar Argentina a ranar talala mai zuwa.


Like it? Share with your friends!

-1
210 shares, -1 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like