Rikicin Iran da Amurka: Buhari ya gana da shugaban NNPC


Shugaban kasa Muhammad Buhari ya yi wata ganawar sirri da,Mele Kyari shugaban kamfanin mai na kasa NNPC a fadar Aso Rock dake Abuja.Kamfanin dillancin labarai na NAN ya rawaito cewa babu wani cikakken bayani kan dalilin ganawar.NAN ya rawaito cewa ganawar na zuwa ne lokacin da ake tsaka da tashin hankali tsakanin kasar Amurka da Iran bayan kisan kwamandan sojan kasar Iran, Qassem Soleimani da kuma harin ramuwar gayya da Iran ta kai kan sansanin sojojin Amurka dake Iraki.Har ila yau kamfanin dillancin labaran ya rawaito cewa a wani lokaci anan gaba ranar Laraba shugaban kasar wanda shine ministan mai zai gana da karamin ministan man fetur,Timipre Sylva.A halin yanzu dai farashin danyen mai ya yi sama a kasuwar duniya tun bayan harin na Amurka.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like