Rikicin APC: Gwamnoni 13 sun gana da Buhari


Gwamnonin jam’iyar APC sun yi wata ganawar sirri da shugaban kasa, Muhammad Buhari a fadar shugaban kasa dake Abuja kan rikice-rikicen da suka dabaibaye jami’yar.

Taron ya kuma samu halartar mataimakin shugaban kasa,Yemi Osinbajo da kuma shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa,Abba Kyari.

Gwamnonin sun halarci taron karkashin jagorancin,Atiku Bagudu shugaban kungiyar gwamnonin jam’iyar APC.

Sauran gwamnonin da suka halarci taron sun hada da Nasir el-Rufai (Kaduna), Babajide Sanwo-Olu (Lagos), Dapo Abiodun (Ogun), Gboyega Isiaka (Osun), Godwin Obaseki (Edo), Babagana Zulum (Borno), Simon Lalong (Plateau), Inuwa Yahaya (Gombe), Kayode Fayemi (Ekiti), Abdullahi Sule (Nasarawa), Abubakar Badaru (Jigawa), da kuma Sani Bello (Niger).

Mataimakin gwamnan jihar Kano,Nasiru Yusuf Gawuna da kuma na jihar Kogi, Edward Onoja na daga cikin wadanda suka halarci taron.

Taron da aka fara karfe uku na rana an kammala shi da karfe hudu da rabi na yamma dukkanin gwamnonin da mataimakansu sun ki cewa komai kan abin da suka tattauna a taron.
Amma kuma wasu majiyoyi sun bayyana cewa taron baya rasa nasaba da rikicin jam’iyar da ya addabi reshenta na jihar Edo inda shugabanta, Adam Oshiomhole ya fito.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like