Rikicin APC: Ana zargin wasu gwamnonin jam’iyar da kunnowa Oshiomhole wuta


Shugabannin jam’iyyar APC na jihohi 36 sun fadawa shugaban kasa Muhammad Buhari cewa wasu daga cikin gwamnonin jam’iyar sune suke son cire shugaban jam’iyyar na kasa, Adams Oshiomhole saboda bukatar zaben shugaban kasa na 2023.

Matsayar shugabannin na kunshe ne cikin wani jawabin bayan taro da aka rubuta wanda jagoran shugabannin jam’iyar na jihohi wanda shine shugaban jam’iyyar reshen jihar Borno ya sanyawa hannu bayan ganawarsu da shugaban kasa Buhari a fadar Aso Rock dake Abuja.

A cikin jawabin bayan taron shugabannin sunyi zargin cewa wasu daga cikin gwamnonin sunyi wa jam’iyar zagon kasa a zaben gwamnonin jihohin Kogi da Bayelsa domin su dorawa shugaban jam’iyyar laifin da za a cire shi.

Sun kuma yi kira ga shugaban kasa Muhammad Buhari da yaja hankalin da suke kokarin tayar da rikici a jam’iyar a lokacin da ya kamata a hada wannu wajen ciyar da ita gaba.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like