Cikin wani sakon da ya nemi kakafen labarai su watsa cikin gaggawa, hafsan soji mafi girman mukami a kudancin Afghanistan Janar Sami Sadat, ya ce za su fuskanci “yan Taliban domin su fatattake su ta ko halin kaka daga yankin. Saboda hake ya nemi mazauna Lashkar Gah da su kaurace wa matsugunansu.

Dama dai Ofishin Jakadancin Majalisar Dinkin Duniya a Afghanistan ya bayyana damuwa a shafinsa na Twitter dangane da halin da fararen hular garin ke ciki, yana mai kira da “a gaggauta kawo karshen fada a cikin birane. sai dai kakakin ma’aikatar tsaron Afganistan, Fawad Aman, ya ce jiragen yakin Amirka sun kai hare -hare a Lashkar Gah, ba tare da sojojin Amurka a Afghanistan sun yin tsokaci a kai ba.

Tun dai bayan da Amirka ta bayyana aniyar kakkabe hannayenta daga harkar tsaro a kasar Afghnaistan, ‘yan Taliban da ke da tsattsauran ra’ayin addini ke mamaye garuruwa da dama na kasar.