Rikici ya barke a taron APC na Ogun


Jami’an tsaro sun yiwa shugaban kasa Muhammad Buhari kawanya dai-dai lokacin da rikici ya barke a wurin taron gangamin yakin neman zaben jam’iyar APC a jihar Ogun.

Taron gangamin yakin neman zaben ya gudana ne a filin wasa na MAKO Abiola dake garin Abeokuta babban birnin jihar inda aka samu cincirindon al’umma.

Taron ya zo karshe ba shiri lokacin da Buhari ya daga hannun dantakarar gwamnan jihar karakashin jam’iyar APC, Dapo Abiodun.

Shugaban kasar yana daga hannun Abiodun sai wasu fusatattun yan jam’iyar suka shiga jefa abubuwa ya zuwa inda yake abinda ya tilastawa jami’an tsaro yi masa zobe.

Tunda fari fusatattun magoya bayan jam’iyar sai da suka jefi shugaban jam’iyar,Adams Oshimhole lokacin da yake jawabi tare da korar magoya bayan Abiodun daga filin wasan.


Like it? Share with your friends!

1
55 shares, 1 point

Comments 1

Your email address will not be published.

You may also like