Rikici da ‘yan shi’a ya tilastawa majalisar wakilai dage zamanta


Mambobin majalisar wakilai ta tarayya sun yi gaggawar dage zamansu na yau bayan da yan kungiyar yan uwa musulmi ta Najeriya da akafi sani da shi’a suka kutsa kai harabar majalisar kasa abin da ya jawo arangama tsakaninsu da jami’an tsaro.

Femi Gbajabiamila shine ya sanar da haka inda ya ce yan majalisar sun dage zamansu saboda barazanar tsaro.

Yan kungiyar ta shi’a sun fasa kofar farko ta shiga majalisar inda suka cigaba zuwa kofa ta biyu wacce daga ita sai ginin majalisar.

Amma kuma jami’an tsaro dake girke a majalisar sun dakile zanga-zanga ta hanyar harba bindiga sama domin wargaza masu zanga-zangar.

Yan kungiyar na zanga-zanga ne kan cigaba da tsare shugabansu, Sheikh Ibrahim Elzakzaky.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like