Rijiya Ta Hadiye Mutane Hudu A Yayin Da Suke Gyaranta


Wani abun al’ajabi ya faru a ƙaramar hukumar Yabo a Unguwar Baici, inda wasu mutane hudu masu gyaran rijiya suka yi batan-dabo a rijiyar a yayin da suke gyaran ta.

Wadannan mutane hudu sun fara aikin gyaran rijiyar ne tun karfe tara na safiyar yau kuma har yanzu ba su fito daga rijiyar ba, kuma an neme su a cikin rijiyar an rasa.

Mutane da dama a garin na Yabo sun garzaya wajen da lamarin yake faruwa don ganewa idanun su abin al’jabin da ya auku.


Like it? Share with your friends!

1
70 shares, 1 point

Comments 1

Your email address will not be published.

You may also like