Mutum kimanin arba’in da hudu aka tabbatar sun mutu a wani turmutsutsu da aka samu a wajen ibadar Yahudawa a Isra’ila. Wasu rahotanni sun sheda cewa, wani dandamali ne ya rufta, lamarin da ya haifar da cunkoson da ya janyo ana tattake jama’a har da dama suka rasa rayukansu wasu daruruwa suka ji rauni. 

Wani da ya tsira da ransa, ya yi karin bayani kan munin lamarin yana mai cewa: ”Abin ya soma da ture-reniya bayan mintuna ashirin sai lamura suka rincabe, mutane suka fara faduwa ana tattake jama’a ga rashin iska, wasu na ta ihu wasu na cewa ba sa iya numfashi akwai  wadanda ko ihu sun kasa yi, gaskiya abin ba kyau.”

Dubban Yahudawa mabiya addinin gargajiya ne ke gudanar da wannan taron ibadar a duk shekara, a tsaunin nan mai suna Meron, a taro mafi tsarki a wurin Yahudawan duniya. Firaiministan Isra’ila Benjamin Netanyahu, ya baiyana lamarin a matsayin babban bala’i da ya afkawa kasar. A daren jiya Alhamis aka soma gudanar da taron da aka soke a bara a saboda annobar corona amma aka gudanar da shi a wannan shekarar duk da jan kunnen mahukunta kan mutunta ka’idojin hana yaduwar cutar a lokacin taron da ke hada kan dubban Yahudawa.