Shugaban kasa, Muhammad Buhari ya amince ya gabatar da jawabi gaban majalisar wakilai ta tarayya,a cewar Femi Gbajabiamila shugaban majalisar.

Majalisar wakilan ta gayyaci shugaban kasar domin yayi mata jawabi kan kashe-kashen da suke faruwa a sassa daban-daban na kasarnan.

Da yake magana a fadar shugaban kasa ranar Laraba, Gbajabiamila ya ce ya gana da shugaban kasa ne kan batun.

Gbajabiamila ya fadawa yan jaridar dake fadar shugaban kasa cewa an tsayar tare da amincewa da ranar da shugaban zai yi jawabin kuma nan ba da jimawa ba za a sanar da ranar.