Rashin kyawun yanayi ne ya jawo hatsarin jirgin Osinbajo


Jirgin da yake ɗauke da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo daga Abuja zuwa garin Kabba a jihar Kogi ya fadi dai-dai lokacin da yake sauka sakamakon rashin kyawun yanayi.

Kamfanin Caverton Helicopters da suka mallaki jirgin sune suka bayyana haka cikin wata sanarwa da suka fitar ranar Asabar.

Osibanjo na kan hanyarsa ne ta zuwa yakin neman zabe jihar Kogi lokacin da jirgin da yake ciki ya yi hatsarin a garin na Kabba lokacin da yake shirin sauka.

Babu asarar rayuka ko kuma jikkata da aka samu yayin hatsarin.

Mataimakin shugaban kasar ya fito daga jirgin ba tare da ko kwarzane ba kana ya ci-gaba da yin abinda ya kai shi jihar inda ya samu kyakkyawar tarba yayin da ayarin motocinsa ke shiga cikin garin.

Josiah Chisoms, shugaban kamfanin ya bayyana cewa tuni aka kaddamar da binciken musabbabin faruwar lamarin.

“Jirgi mai saukar ungulu samfurin Agusta AW139 dake ƙarƙashin kulawar kamfanin Caverton Helicopters ya gamu da hatsari lokacin da yake sauka a garin Kabba dake jihar Kogi da misalin karfe uku na ranar yau ( 2 ga watan Faburairu, 2019) sakamakon rashin kyawun yanayi da ba kasafai aka fiya samu ba ya ce,”

Sanarwar ta kara da cewa babu wani fasinja ko kuma ma’aikacin jirgin da ya jikkata sakamakon hatsarin.


Like it? Share with your friends!

-1
75 shares, -1 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like