Rashin kammala zabe:Osinbajo ya gana da gwamnonin jihohin Bauchi da Adamawa


Mataimakin shugaban kasa,Yemi Osinbajo ya gudanar da wata ganawar sirri a lokuta mabanbanta da gwamnonin jihohin, Bauchi da Adamawa.

Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta,INEC ta ayyana zaben gwamnonin jihohin biyu a matsayin wanda bai kammala ba.

Dukkanin gwamnonin biyu sun ki yarda suyi magana da yan jaridun dake fadar shugaban kasa.

INEC ta saka ranar 23 ga watan Maris a matsayin ranar da za a gudanar da zaben gwamnonin da ba a kammala ba a jihohin Adamawa,Benue, Plateau,Sokoto Bauchi,Kano.

Idan ka ɗauke jihar Plateau inda jam’iyar APC ke kan gaba da yawan kuri’u a dukkanin ragowar jihohin jam’iyar adawa ta PDP ce kan gaba.


Like it? Share with your friends!

-1
96 shares, -1 points

Comments 2

Cancel reply

Your email address will not be published.

You may also like