Rasha Ta Fara Daukar Matakan Karya Darajar Dala A Fadin Duniya


Kasar Rasha ta bayyana cewar ya zama wajibi ga dukkanin kasashe da su dauki matakan rage amfani da dala a cinikayya tsakaninsu.

Mai magana da yawun gwamnatin Rasha Dimitriy Peskov, ya amsa tambayoyin ‘yan jaridu a Moscow babban birnin Rasha inda ya bayyana cewar Rasha, China da Turkiyya sun dauki matakan rage amfani da dala a yayin gudanar da kasuwanci a tsakkaninsu.

Ya kara da cewa domin rage karfin dala a duniya kasashe da dama a fadin duniya na tattaunawa da juna inda suke aminta akan gudanar da kasuwanci a tsakaninsu ta amfani da nau’in kudaden kasashensu maimakon dala.

Peskov ya jaddada cewa a yayinda kasashen Nahiyar Turai, gabashi da gabas ta tsakiya ke kokarin aiyanar da yarjejeniya a tsakaninsu domin rage hakimcin da dala take dashi a duniya, Rasha ta dauki wannan matakin da muhinmanci.


Like it? Share with your friends!

-1
80 shares, -1 points

Comments 1

Your email address will not be published.

You may also like