Ranar Litinin Buhari zai kaddamar da kwamitin jam’iyar APC na yakin neman zaben shugaban


A ranar Litinin mai zuwa ne shugaban kasa Muhammad Buhari zai kaddamar da kwamitin jamiayar APC na yakin neman zaben shugaban kasa.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da daraktan sadarwa na kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa Muhammad Buhari, Festus Keyamo ya fitar.

Keyamo ya ce taron zai gudana ne a wurin taro na International Conference Center dake Abuja.

Ya ce wadanda ake sa ran zasu halarci wurin bikin sune mutanen da aka sanar da sunayensu tunda fari a matsayin wakilai a kwamitin.

Kwamitin yakin neman zaben ya kunshi mutane 70.

Shugaban kasa Muhammad Buhari tare da jagoran jam’iyar APC na kasa Bola Ahmad Tinubu sune zasu jagoranci kwamitin.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like