Wata ‘yar jarida mai binciken kwakwaf da ke tarayar Najeriya Tobore Ovuorie ta ci lambar yabo ta DW kan fadin ‘yancin albarkacin baki na wannan shekarar ta 2021.

Tobore Ovuorie, tana cikin manyan ‘yan jaridu masu binciken kwakwaf da bin diddgi a Najeriya. ‘Yar jaridar tana da burin tsage gaskiya da kuma bankado boyayyun al’amura. 

A shekarar 2013, ta yi kasadar shiga aikin karuwanci na tsawon watanni 7 da nufin bankado da yadda ake safarar mata domin aikin karuwanci da kuma sayar da sassan jiki bil’Adama.

Wannan sai da rai da Ovuorie ke yi ya janyo hankalin shugaban DW Peter Limbourg da kuma ya bata kyautar wannan shekara.