Priyanka Chopra za ta gana da Rahama Sadau


 

sadau

Jarumar fim din hausa da aka dakatar, Rahama Sadau ta kara samun wani gagarumin cigaba a harkar sana’arta ta shirin fim, domin kuwa burinta da ta dade tana mafarki yana daf da cika, kusan a koda yaushe akayi hira da ita a kafafen yada labarai takan fadi cewa “ita ‘yar fim din da tafiso kuma ta keso ta zama kamarta itace, Priyanka Chopra,”wato shahararriyar ‘yar fim dinnan ta kasar Indiya.

To ayaudai hankalin Priyanka yakai kan wata magana da Rahamar tayi wadda take cewa “Saboda irin nasarar da Priyanka ta samu itama abin yana zaburar da ita domin ta zama kamar Priyankar,” Rahama tayi wannan maganane a shafin sada zumunta kuma Prinyankar ta mayarmata da sakon inda tace “Nagode ina fatan haduwa dake nan bada dadewa ba , ina miki fatan samun nasara a dukkan abubuwan da ki kasa a gaba”.

Priyanka dai shahararriyace a finafinan Indiya kuma a yanzu haka ta shiga harkar fina finan kasar Amurka inda acanma tauraruwarta take haskakawa, to saidai wasu nayiwa Priyankar kallon wata fitsararriya a cikin jaruman fim din Indiya wadda bata da kunya.

Wannan kira da Priyanka tayiwa Rahama Sadau ba karamin abin cigaba bane a gareta domin idan za’a iya tunawa a irin ta hakane mawakin kasar Amurka Akon yayi magana da Rahama Sadau inda daga baya ya gayyaceta har can kasar Amurka suka hadu.

 

 

Screenshot_2017-07-06-19-10-42

 

 


Like it? Share with your friends!

-6

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like