Pinnick ya sake lashe zaben kujerar shugaban hukumar kwallon kafar Najeriya


An sake zabar, Amaju Pinnick a matsayin shugaban hukumar kwallon kafar Najeriya ta NFFa karo na biyu.

Shine shugaban hukumar na farko a tarihi da ya lashe zabe har sau biyu.

Pinnick ya lashe zaben da gagarumin nasara inda ya samu kuri’a 34 inda Shehu Maigari ya samu kuri’u 8 ya yin da Taiwo Ogunjobi ya samu kuri’a biyu, sai Chinedu Okoye da ya gaza samun kuri’a.

Haka kuma Seyi Akinwumi ya sake komawa kan kujerarsa ta mataimakin shugaban hukumar kwallon kafar.


Like it? Share with your friends!

1
93 shares, 1 point

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like