Hukumar da ke kula da zaben ta bayyana sakamakon ne wata daya da rabi bayan zaben. Ta kuma ce Pedro Castillo ya zarta abokiyar adawarsa da kuri’u dubu 44. Tun farko Keiko Fujimori ‘yar Alberto Fujimori tsohon shugaban na Peru da aka yanke wa hukuncin daurin shekaru 25 na zaman gidan yari saboda samunsa da laifin cin hanci,ta yi watsai da sakamakon zaben  da ta ce an yi arringizon kuri’u, ta kuma shigar da kara amma kotu ta kori karan.