PDP ta yi watsi da sakamakon zaben gwamnan jihar Ekiti


Jam’iyar PDP ta yi watsi da sakamakon gwamnan jihar Ekiti da ya bawa jam’iyar PDP nasara.

Kayode Fayemi dantakarar jam’iyar APC shine ya kayar da Kolapo Olusola ɗan takarar jam’iyar PDP me mulkin jihar.

Dantakarar na jam’iyar APC ya lashe zaɓen da ƙuri’u 197459 ya yin dantakarar jam’iyar PDP ya samu ƙuri’u 178,121.

Da yake magana da yan jaridu ranar Lahadi, Kola Olagbondiyan mai magana da yawun jam’iyar ya ce a zahirance dantakararsu ne ya yi nasara idan aka yi la’akari da sakamakon da aka tattara daga dukkanin mazabu dake jihar.

“Baza a iya murkushe jam’iyar PDP ba,PDP tayi watsi da sakamakon gabaki daya da APC, jami’an tsaro da kuma INEC suka kirkira,”Kola Olagbondiyan ya ce.

“Jam’iyar tayi watsi da sakamakon da aka jirkita da kuma bayyana Fayemi da aka yi a matsayin wanda ya lashe zaben.”


Like it? Share with your friends!

2
84 shares, 2 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like