PDP ta nemi a sake kidayar kuri’un zaben gwamnan jihar Kaduna


Isah Ashiru,dan takarar gwamnan jihar Kaduna a karkashin jam’iyyar PDP a zaben da ya gabata ya bukaci a sake kirga kuri’un da aka kada a daya bayan daya a zaben gwamnan jihar.

Hakan ne kunshe ne cikin bukatar da,Elisha Kurah lauyan dantakarar jam’iyar ta PDP da ya shigar gaban kotun sauraron kararrakin zabe dake zamanta a Kaduna.

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa,ta ayyana Mallam Nasiru El-rufai dantakarar jam’iyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben da kuri’u 1,045,427 ya yin da babban abokin hamayyarsa na jam’iyar PDP,Isa Ashiru wanda ya samu kuri’u 814,168.

Da yake magana da manema labarai bayan wani zaman kotu gabanin fara sauraran shari’ar,Kurah ya ce ya nemi kotun da ta umarci INEC ta sake kirga kuri’un saboda yawancin sakamakon kuri’un da aka bayyana bayan zaben bana gaskiya bane.

Ya ce sakamakon sake kirga kuri’un zai tabbatar da cewa PDP ce ta lashe zaben kujerar gwamnan jihar.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like