PDP Ta Dakatar Da Mataimakin Shugaban Jam’iyyar Na Shiyyar Arewa Bisa Zargin Goyon Bayan Buhari


Jam’iyyar PDP ta dakatar da mataimakin jam’iyyar na kasa, na Arewa, Babayo Gamawa, saboda zargin sa da yin sakaci da aiki da kuma yi wa jam’iyyar yankan-baya.

Sakataren Yada Labarai na Kasa na PDP, Kola Ologbondiyan ne ya bayyana cewa Babban Kwamitin Zartaswa na PDP ne ya dakatar da Gamawa.

Kwamitin ya yi taron gaggawa ne a ranar 5 Ga Janairu, inda aka tattauna korafe-korafen da aka rika gabatarwa a kan Gamawa.

An samu rahotannin ficewar wasu daga PDP zuwa APC a Kano.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like