PDP Sun Ƙulla Abota da Sabuwar Jam’iyyar APC Inda Suka Canza Suna Zuwa CUPP


Jam’iyyar Peoples Democratic Party, PDP, a yau Litinin, 9 ga watan Yuli ta hade da jam’iyyun siyasa sama da guda 30 ta sanar da sabon sunanta a matsayin jam’iyyar Coalition of United Political Parties (CUPP).

A cewar gidan talbijin din Channels, sanarwar na zuwa ne bayan kulla yarjejeniyar fahimta da shugabannin jam’iyyun da suka hade suka yi.

Hakan duk kokari ne na son ganin sun kayar da jam’iyyar APC, mai mulki a zaben 2019 mai zuwa.

Jam’iyyun da suka halarci taron sun hada da African Democratic Congress (ADC), Social Democratic Party of Nigeria (SDP), National Conscience Party (NCP), Labour Party, da sauran sabbin jam’iyyun da aka yiwa rijista.

Shugaban jam’iyyar APC na kasa Uche Secondus, tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, tsohon shugaban majalisar dattawa David Mark, shugaban kungiyar R-APC, da kuma Sanata Dino Melaye na daga wadanda suks halarci taron.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like