PDP na buƙatar Saraki, Kwankwaso su dawo cikin jam’iyar da gaggawa


Walid Jibrin shugaban kwamitin amintattu na jam’iyar PDP  yayi kira ga shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki da kuma tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da su gaggauta dawowa cikin jam’iyar.

Jibrin, a ranar Talata ya bayyana sake dawowar tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, cikin jam’iyar a matsayin wani abin alkhairi ga jam’iyar.

“Muna kuma sa ran dawowar wasu daga cikin tsofaffin gwamnoninmu, yan majalisar kasa da kuma wasu fitattun magoya bayan jam’iyar,”ya bayyana haka lokacin da wata kungiya mai suna kungiyar PDP Ward2Ward  wadanda suka kai masa ziyara a Abuja.

“Idan haka ta tabbata to jam’iyar zata tsaya car da ƙafafuwanta.

“Zamu cigaba da karawa duk wanda suka barmu kwarin gwiwar dawowa su sake hadewa damu.

“Saboda haka muke kiran Saraki, Kwankwaso da kuma dukkanin tsofaffin yan jam’iyar PDP  dake majalisa wadanda suka fice daga jam’iyar da su dawo da gaggawa.”

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like