Patience Jonathan ta kasance tana daukan albashi dubu dari 700 a wata duk da ta bar aiki – EFCC


Hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) a ranar Litinin, 13 ga watan Mayu tayi zargin cewa Dame Patience Jonathan, uwargidar tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan ta ci gaba da karban albashinta na N700, 000 duk wata, watanni bakwai bayan tayi ritaya a matsayin ma’aikaciyar gwamnati.

An rawaito cewa tsohuwar uwargidar Shugaban kasar, wacce tayi ritaya daga ma’aikatar gwamnatin Bayelsa a matsayin sakatariyar din-din-din a ranar 14 ga watan Oktoba, 2014 ta ci gaba da karban albashi har zuwa watan Mayun 2015, lokacin da mijinta ya bar kujerar mulki.

Hukumar ta bayyana hakan ne a gaban babbar kotun tarayya da ke Lagas a lokacin zaman shari’a na kwace dukiyar uwargidar Jonathan da ke gaban kotun.

Hukumar na rokon kotun da ta yi umurnin kwace wasu kadarori na $8.4 million da naira biliyan 7.4 na karshe da ake zargin mallakinta ne.

Justis Mojisola Olatoregun taki amincewa da bukatar EFCC na kwace dukiyoyi amma ta umurci bangarorin da su bayar da hujja na fatar baki domin tabbatar da mamallakin kadarorin.

Tace akwai sarkakiya a karar da ke gabanta, inda ta kara da cewa akwai bukatar hujja ta fatar baki domin wanke su.

A ranar 20 ga watan Afrilu da ya gabata ne alkalin tayi umurnin mallaka wa gwamnatin tarayya kadarorin na wucin-gadi.

An dage sauraron shari’an zuwa ranar 24 ga watan Mayu da misalin karfe 11 na safe.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like