Patience Jonathan ta gana da Aisha Buhari


Patience Jonathan,uwargidan tsohon shugaban kasa, Gudluck Jonathan, ta ziyarci Aisha Buhari a fadar Aso Rock dake Abuja ranar Litinin.

Rahotanni sun bayyana cewa Aisha ta tattauna wasu batutuwa da matar tsohon shugaban kasar ciki har da batun shiga mata harkar siyasa da kuma damawa da su a sha’anin mulki.

Ganawar tasu ta zo ne kasa da mako biyu bayan da tsohon shugaban kasa, Gudluck Jonathan ya gana da Buhari.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like